Isa ga babban shafi
Amurka

Majalisar Dattawan Amurka ta amince da sabuwar dokar rage haraji

Majalisar dattawan Amurka ta amince da sabuwar dokar rage haraji a kan manyan kamfanoni, daya daga cikin alkawurran da Donald Trump ya dau a lokacin yakin neman zabensa.

Donald Trump Shugaban Amurka
Donald Trump Shugaban Amurka REUTERS/Joshua Rob
Talla

Shirin ya nuna cewar za a ragewa kamfanoni kudaden da suke biya daga kashi 35 zuwa kashi 20.

Shugaba Trump ya bayyana shirin da ake amfani da shi da ya gada a matsayin wanda ya hana samun ci gaban tattalin arziki, inda ya bayyana na sa a matsayin gagarumin shirin jam’iyyar Republican.

Trump ya kuma bayyana shirin a matsayin wani juyin-juya halin da zai amfanar da matsakaitan ma’aikata a dai-dai lokacin da ake samun karuwar kamfanonin da suke kwarara zuwa Amurka.

Yan majalisar dattawa 51 ne suka amince da dokar yayin da 48 suka nuna rashin amincewa da shirin, wanda zai sa Amurka ta yi asarar sama da dala triliyan 1 da rabi sakamakon zaftaren haraji

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.