Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka ta samu tsamin dangantaka da Pakistan

A wani yanayi na nuna bacin ranta, Pakistan ta kira jakadan Amurka bayan shugaba Donald Trump ya yi ma ta barazanar rage tallafin da ta ke samu daga kasarsa saboda zargin ta da bai wa ƴan ta’adda mafaka.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump 路透社。
Talla

A cikin daren da ya gabata ne gwamnatin Pakistan da ta fusata da kalaman Trump ta bukaci David Hale, jakadan Amurka a kasar da ya bayyana a gaban ma’aikatar harkokin wajen ƙasar.

Mai Magana da yawun ofishin jakadancin na Amurka ya tabbatar cewa, Mr. Hale ya gana da ma’aikatar amma bai yi ƙarin bayani ba game da ganawar.

Amurka na zargin Pakistan da bai wa ƴan ta’adda mafaka , abin da ya haifar da sabon tsamin dangantaka tsaƙanin ƙasashen biyu.

Firaministan Pakistan, Shahid Khaqan Abbasi ya kira wani taron kwamitin tsaron ƙasar da ya samu halartar manyan hafsoshin soji da jami’an gwamnati don tattanawa kan wannan batu.

A sakon da ya aika a kafar Twitter, shugaba Donald Trump ya ce, Amurka ta bai wa Pakistan kudaden da suka zarce Dala biliyan 33 a matsayin tallafi cikin shekaru 15, amma a cewarsa, babu abin da Pakistan ta saka mu su da shi illa ƙare-rayi da yaudara.

Trump ya ce, Pakistan ta mayar da shugabannin Amurka tamkar wawaye.

Sai dai a martaninta, Pakistan cewa ta yi, ta taimaka wa Amurka kwarai wajen murkushe mayakan Al-Qaeda, amma a yanzu Amurka na caccakar ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.