Isa ga babban shafi
Amurka

Akwai yiwuwar Winfrey ta tsaya takarar shugabancin Amurka

Zazzafaar muhawara ta kaure a Amurka bayan rade-radin da ke cewa, akwai yiwuwar fitacciyar mai gabatar da shirin Talabijin, Oprah Winfrey ta tsaya takarar shugabancin kasar a shekarar 2020 don fafatawa da shugaba Donald Trump.Tuni wasu daga cikin mambobin Jam’iyyar adawa ta Democrat suka yi madalla da Winfrey mai shekaru 63.

Oprah Winfrey a bikin karrama jaruman fina-finai da masu gabatar da shirin talabijin na Golden Globe
Oprah Winfrey a bikin karrama jaruman fina-finai da masu gabatar da shirin talabijin na Golden Globe REUTERS/Lucy Nicholson
Talla

Oprah Winfrey, attajira da aka haifa cikin talauci kafin daga bisani ta shahara a fannin gabatar da shirin talabijin, ba kasafai ta ke fitowa fili don bayyana wata aniya ba, yayin da ta sha kiranye-kiranyen tsayawa takarar shugabancin Amurka.

Rade-radin tsayawarta ya dada karade Amurka ne bayan wani jawabi da ta gabatar a bikin karrama jaruman fina-finai da masu gabatar da shirin talabijin da aka gudanar a karshen mako.

Kafar talabijin ta CNN ta rawaito cewa, wasu makusantanta sun tabbatar da kudirinta na neman shugabancin Amurka, yayin da dadadden abokin zamanta, Stedman Graham ya kara rura wutar rade-radin a hirarsa da jaridar Los Angeles Time, in da ya ce, babu makawa za ta tsaya takara.

A bara dai, Winfrey ta yi watsi da wannan zance na tsayawa takara, yayin da jawabinta na ranar Lahadi a bikin na Golden Globe ya farfado da shaukin hadin kai da fata na gari da kuma sanya mata a cikin lamuran siyasa, abin da masharhanta ke kallo a matsayin kalubalantar gwamnatin Washington duk da cewa ba ta ambaci sunan Donald Trump karara ba.

A martanin da ya mayar, shugaba Donald Trump ya ce, ya san Winfrey sosai kuma ba ya zaton za ta kalubalance shi a shekarar 2020.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.