Isa ga babban shafi
MDD

Yau ce ranar dazuka da itatuwa ta duniya

Yau ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware don nazari game da muhimmancin dazuka da itatuwa wajen inganta muhallan rayuwar al’umma a sassan duniya.Bikin na bana na zuwa ne a yayin da hukumar bunkasa ayyukan gona ta Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci dasa bishiyoyi a birane, lura da cewa, sama da rabin al’ummr duniya na rayuwa ne a biranen.

Dazuka da bishiyoyi na taka rawa wajen magance gurbatar muhalli a duniya
Dazuka da bishiyoyi na taka rawa wajen magance gurbatar muhalli a duniya REUTERS/Kacper Pempel /File Photo
Talla

A yayin da ake bikin ranar dazuka da itatuwa ta duniya, Hukumar bunkasa ayyukan gona ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, nanda shekarar 2050, kusan kashi 70 na duniya zai koma birni.

Kawo yanzu dai, birane sun mamaye kashi uku cal ne na doran kasa, amma kuma a biranen ne ke amfani da kashi 78 na makamashi tare da fitar da kashi 60 na hayaki mai gurbata muhalli a duniya.

Sai dai hukumar bunkasa ayyukan gonan ta ce, mutane da dama na nuna kwazo wajen ganin an cimma burin samar da tsaftataccen muhallin rayuwa nan gaba a kasashen duniya.

Simone Borelli, shi ne babban jami’an kula da dazuka na hukumar bunkasa ayyukan gonar, ya kuma yi karin bayani game da muhimmancin itatuwa a muhallan jama’a, in da ya ce, "Tsaftataccen muhalli, shi ne wanda ke kunshe da itatuwa da dazuka da sauran shuka, wadannan itatuwa na taka rawa wajen inganta muhallan rayuwar al’umma, musamman ta fannin kiwon lafiya. Itatuwa na hana gurbacewar muhalli, kazalika suna iya samar da wuraren shakatawa da wasannin motsa jiki, in da mutane za su iya samun ingantacciyar rayuwa har su yaki matsalar cututtukan da ke da nasaba da zuciya".

Masana na cewa gurbacewar muhalli ne ke haifar da sauyin yanayin da ke haddasa ambaliyar ruwa da zabtarewar laka, abin da ke sanadin mutuwar mutane da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.