Isa ga babban shafi
Syria

Ayarin 'yan tawaye mafi girma ya fice daga gabashin Ghouta na Syria

Ayari mafi girma na mayakan ‘yan tawaye da fararen hula ya isa arewa maso yammacin Syria a yau Talata bayan ficewarsa daga yankin gabashin Ghouta. A baya-bayan nan dai mabanbantan Ayari na ci gaba da ficewa daga yankin na gabashin Ghouta da kuma wajen birnin Damascus karkashin yarjejeniyar ficewa salin alin tsakaninsu da dakarun gwamnati.

Yanzu haka dai adadi mafi girma ya fice daga biranen Arbin da Zamalka da kuma wani yanki na Jobar da ke  karkashin ikon Faylaq al Rahman.
Yanzu haka dai adadi mafi girma ya fice daga biranen Arbin da Zamalka da kuma wani yanki na Jobar da ke karkashin ikon Faylaq al Rahman. REUTERS/ Khalil Ashawi
Talla

Sama da wata guda kenan dai dakarun gwamnatin Syria da ke samun goyon bayan Rasha da wasu ‘yan tawayen suka kaddamar da munanan hare-hare da zimmar karbe yankin Ghouta da ke wajen birnin Damascus.

Dakarun sun yi nasarar karbe sama da kashi 90 na yankin, yayin da kuma suke ci gaba da kokarin kawar da tsirarun mayakan da suka saura a yankin ta hanyar zaman tattaunawa karkashin jagorancin Rasha.

Makamanciyar wannan tattaunawa ta yi tasiri wajen kwashe dubban ‘yan tawaye da iyalansu har ma da fararen hula daga Ghouta zuwa Lardin Idlib.

Yanzu haka dai adadi mafi girma ya fice daga biranen Arbin da Zamalka da kuma wani yanki na Jobar da ke karkashin ikon Faylaq al Rahman.

Wannan kungiya ta cimma wata matsaya da gwamnatin Moscow a ranar Jumma’ar da ta gabata, in da aka fara aiwatar da ita a safiyar ranar Asabar bayan kusan mutane dubu 1 sun fice nan take.

Tun daga wannan lokaci ne kuma aka ci gaba da samun adadi mai yawan gaske da ke kaurace wa yankin, in da kawo yanzu aka samu mutane sama da dubu 6.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.