Isa ga babban shafi
Syria-Turkiya

Turkiyya za ta fara kai farmaki Manbij

Shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan ya ce ya na gab da fadada hare-haren da ya ke kaiwa kan 'Yan tawayen Kurdawa na Syria matukar suka ki amincewa da fita daga garin Manbij, da ke gabashin birnin Damascus karkashin yarjejeniyar da ke tsakaninsu da Majalisar tsaron kasar ta Syria.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan ya sha alwashin fadada hare-haren da dakarun sojinsa ke kaiwa wasu yankunan na kasar Syria da ke hannun mayakan 'yan tawaye.
Shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan ya sha alwashin fadada hare-haren da dakarun sojinsa ke kaiwa wasu yankunan na kasar Syria da ke hannun mayakan 'yan tawaye. REUTERS/Umit Bektas/File Photo
Talla

Kalaman na shugaba Racep Tayyib Erdogan na zuwa ne a dai dai lokacin da dakarun sojin Syria da hadin gwaiwar na Rasha ke ci gaba da samun nasarar kwace manyan sassan da ke hannun 'yan tawayen Syria a baya.

Erdogan dai yanzu haka ya kwace iko da yankin Afrin bayan fatattakar mayakan da ke iko da yankin yayinda ya sha alwashin fadada hare-haren da Turkiyya ke kai wa yankunan 'yan tawaye.

Garin Manbij dai yanzu haka na mamaye da dakarun sojin da Amurka ta girke matakin da ka iya zama babbar barazana ga Turkiyya musamman idan ta yi yunkurin kai hare-hare da nufin kwace yankin.

Turkiyya, Rasha da kuma Iran su ne kasashe 'yan gaba-gaba da ke fatattakar 'yan tawayen daga sassa daban-daban na Syria, yayinda a bangare guda Turkiyya ta fi mayar da hankali kan 'yan tawayen Kurdawa na YPG wadanda ta bayyana da kungiyar ta'addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.