Isa ga babban shafi
Iraqi

An kada kuri'a karon farko a Iraqi bayan kammala yakar ISIS

Jami’an tsaro a kasar Iraqi sun jefa kuri’a a karon farko tun bayan da aka fara yaki da kungiyar ISIS a cikin kasar. Dama an shata bari jami’an tsaron kasar su fara jefa kuri’a akalla kwanaki 2 kamin zaben na ‘yan Majalisu a ranar Assabar.

Ko a birnin Basra da ke a yankin kudancin kasar ma an ga dimbin jami’an tsaro da suka jefa kuri’u da alamun Tawada a yatsunsu.
Ko a birnin Basra da ke a yankin kudancin kasar ma an ga dimbin jami’an tsaro da suka jefa kuri’u da alamun Tawada a yatsunsu. SAFIN HAMED / AFP
Talla

Al’ummar kasar Iraqi dai na cike da fatar ganin zaben da za’a gudanar ya kawo karshen shekaru 15 da aka yi ana zubar da jini a cikin kasar tun bayan hambarar da gwamnatin shugaba Saddam Hussein.

Yanzu haka dai aikin sake gina kasar ne babban abinda hukumomin kasar da ma daidaikun al’umma suke shaukin ganin ya faru.

Wani jami’in dan sanda Khalid Renan da ke a yankin Mosoul inda yakin yayi kamari a baya, da kuma aka kwace daga hannun ‘yan IS a cikin watan Yuli, ya ce babbar fatarsu it ace su gudanar da zabe don amfanin ‘ya’yansu nan gaba.

Rahotanni na nuni da yadda aka tsaurara matakan tsaro a sassan kasar da dama, bayan da aka samu labarin cewar IS na shirin kaddamar da kai wasu hare-hare a lokacin zaben.

Ko a birnin Basra da ke a yankin kudancin kasar ma an ga dimbin jami’an tsaro da suka jefa kuri’u da alamun Tawada a yatsunsu.

Ya zuwa yanzu dai an bayyana addadin wadanda suka yi rajistar yin zaben su sama da Miliyan 24 a cikin kasar, da kuma Karin wasu kimanin miliyan 1 da za su jefa kuriunsu a kasashen ketare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.