Isa ga babban shafi
Amurka-Korea

Za a ga tasirin yarjejeniyarmu da Korea ta Arewa kafin 2020 - Amurka

Amurka ta ce tana da kwakkwarar zato cewa yarjejeniyar da ta kulla kan rage ayyukan makaman nukiliyar Korea ta Arewa za ta yi tasiri kafin karshen wa'adin farko na shugaba Donald Trump a shekarar 2020.

Masu adawa da zaman fahimtar jumnan na cewa ganawar bata tsinana komi ba tunda babu wata kwakkwarar mataki da aka dauka a zahiri da kowa zai gani.
Masu adawa da zaman fahimtar jumnan na cewa ganawar bata tsinana komi ba tunda babu wata kwakkwarar mataki da aka dauka a zahiri da kowa zai gani. Reuters/路透社
Talla

Da yake Magana a karon farko bayan ganawa gaba-da-gaba tsakanin Donald Trump da Kim Jong Un a Singapore, Sakataren waje na Amurka Mike Pompeo ya fadawa manema labarai a Seoul na Korea ta kudu wadda ta shiga tsakani cewa bai fidda tsammanin nasara ba cikin shekaru biyu da rabi da suka rage wa Trump.

Mike Pompeo ya bayyana cewa akwai sauran aiki sosai bayan zaman fahimtar juma da aka yi.

Ganawar Trump da Kim mai dimbin tarihi karon farko, sun bayyana cikin sanarwar bayan taron cewa sun amince suyi aiki don wargaza dukkan shirin nukiliya Korea ta Arewa.

Masu adawa da zaman fahimtar jumnan na cewa ganawar bata tsinana komi ba tunda babu wata kwakkwarar mataki da aka dauka a zahiri da kowa zai gani.

Yau Alhamis ne dai Sakataren Wajen na Amurka Mike Pompeo zai gana da takwaransa na Korea ta kudu, da na Japan duk dai don ya karfafa masu guiwa game da tattaunawar da Trump yayi da Shugaba Kim na Korea ta Arewwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.