Isa ga babban shafi
Faransa

Ana bincike kan kudin tallafa wa Macron a Faransa

Wani Mai Gabatar da kara a Faransa ya kaddamar da bincike kan zargin cewar hukumomin karamar hukumar Lyon sun bai wa shugaba Emmanuel Macron tallafin kudade ta hanyar da ba ta kamata ba lokacin yakin neman zabensa a bara.

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron LUDOVIC MARIN / POOL / AFP
Talla

Bayanai sun ce an kaddamar da binciken kan shugaba Macron ne sakamakon wani korafi  da wani dan majalisa da ke Lyon ya yi a makon jiya cewar, hukumomin yankin sun taimaka wa shugaban wanda ya yi yakin neman zabe sau da dama a can garin na Lyon.

Wanda ya gabatar da zargin ya ce, an yi amfani da kudade da kuma jami’an gwamnatin Lyon wajen taimaka wa shugaba Macron wanda hakan ya saba wa dokokin zabe.

Daya daga cikin wadanda suka taimaka wa shugaban shi ne Magajin Garin Lyon, Gerard Collomb wanda tuni shugaba Macron ya nada shi ministan cikin gida bayan nasarar zaben watan Mayun shekarar 2017.

Wani jami’in ministan cikin gidan ya ce, babu wani sabon labari dangane da zargin saboda hukumomin Lyon sun dade suna bayani akai.

Gwamnatin Faransa ta yi doka kan kashe kudaden da 'yan takarar shugaban kasa ke yi, wadda ta ce babu wani dan takarar da zai kashe kudin da ya zarce Dala miliyan 26 a lokacin yakin neman zabe.

Yanzu haka ana tuhumar tsohon shugaban kasar, Nicolas Sarkozy saboda karbar kudaden yakin neman zaben da suka saba ka’ida a shekarar 2007.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.