Isa ga babban shafi
Faransa-India

India ta dara Faransa a karfin tattalin arziki - rahoto

India ta zama kasa ta shidda mafi karfin tattalin arziki a duniya bayanda da ta doke Faransa wadda yanzu ta koma matsayin ta bakwai a wani rahoto da bankin duniya ya fitar yau din nan kan kasashe mafiya karfin tattalin arziki a bana.

Asusun bada lamuni na duniya IMF ya ce tattalin arzikin India zai karu da kasha 7.4 cikin shekarar nan yayinda a shekarar 2019 kuma zai karu da kasha 7.8.
Asusun bada lamuni na duniya IMF ya ce tattalin arzikin India zai karu da kasha 7.4 cikin shekarar nan yayinda a shekarar 2019 kuma zai karu da kasha 7.8. REUTERS/Edgar Su
Talla

Rahoton ya nuna cewa, karfin tattalin arzikin India a ma’aunin GDP na bana ya nuna yadda tattalin arzikin ya kai dala tiriliyan 2.597, yayinda na Faransa ke matsayin Tiriliyan 2.582.

Tattalin arzikin India dai ya rika hauhawa ne tun daga watan Yulin 2017 bayan tabarbarewar da ya fuskanta a baya, wanda ake alakantawa da wasu tsare-tsaren gwamnatin Firaminista Narendra Modi.

Wata kididdiga ta nuna cewa raguwar tattalin arzikin Faransar na da alaka da hauhawar tattalin arzikin India wanda rahoton ke nuna cewa akwai yiwuwar ya kara hauhawa nan gaba kadan.

Karfin tattalin arzikin India dai ya linka ne cikin kasa da shekaru 10 wanda hakan ke nuna yiwuwar ta koma mafi karfin tattalin arziki a Asia a dai dai lokacin da tattalin arzikin China ke fuskantar koma baya.

Asusun bada lamuni na duniya IMF ya ce tattalin arzikin India zai karu da kasha 7.4 cikin shekarar nan yayinda a shekarar 2019 kuma zai karu da kasha 7.8.

Rahoton dai ya alakanta hauhawar tattalin arzikin kasar da yadda ta mayar da hankali wajen gyara tsarin karbar haraji da kuma bayar da hayar gidaje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.