Isa ga babban shafi
Rahoto

Kifaye sun yi karanci a tekun duniya

Wani sabon rahoton Majalisar Dinkin Duniya na nuna matukar fargaba game da karancin kifaye a manyan teku na duniya duk da cewa mabukata cin-kifi da ke gina jiki na kara yawa. Rahoton na ganin kasashe masu tasowa na da gagarumin aiki don wadata kasashensu da wannan nau’in abinci.

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi kan karancin kifi a duniya
Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi kan karancin kifi a duniya Oliver Lucanus/Belowwater.com
Talla

Manuel Barange, Daraktan Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya mai kula da bangaren kifi, ya shaida wa Asusun Thomas Reuters cewa, idan aka yi sakaci,  kasashen nahiyar Afrika za su rika sayo kifi daga kasashen duniya domin tsadar kifin nan gaba wanda zai shafi marasa karfi.

A cewar Daraktan,  Afrika na da dukkan abin da ya dace ta samar da wadataccen kifi a nahiyar amma sai ta samu tallafin kudade da abincin da kifayen ke bukata.

Rahoton na nuna cewa, kiwon kifi na daga cikin sana'o'i masu saurin habbaka cikin shekaru 40 da suka gabata.

Wannan rahoto ya ce, ganin yadda ake samun karancin kifaye a manyan teku na duniya, wasu kasashen na lmayar da hankali kan samar da kifin, domin kasashen Afrika kamar Algeria wadda Gwamnatinta ke taimaka wa manoman kifi sosai.

A yanzu haka, mutanen duniya biliyan 3 da dubu 100 na dogaro ne ga cin kifi don ba su kashi 20% cikin 100 na abinci mai gina jiki da suke bukata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.