Isa ga babban shafi
Amurka-China

Trump ya nanata kudirinsa na karin haraji kan kayan China

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce a shirye ya ke ya kara tsananta harajin da ya sanyawa kayakin da China ke shigarwa kasar matukar bukatar hakan ta taso. Trump wanda ke wannan batu a wata zantawarsa kai tsaye da gidan talabijin din kasar ya ce matakan harajin ba su da nasaba da siyasa face ga ci gaban kasar.

China dai ta zargi Amurkan da tada gagarumin yaki na kasuwanci mai cike da tarihin ga tattalin arzikin kasashen duniya.
China dai ta zargi Amurkan da tada gagarumin yaki na kasuwanci mai cike da tarihin ga tattalin arzikin kasashen duniya. REUTERS/Leah Millis
Talla

A cewar shugaban na Amurka Donald Trump china ta jima ta na yaudararsu musamman bayan yarjejeniyar kasuwancin da ta bata damar shigar da kayan dala biliyan 505.5 kasar ta Amurka a shekarar 2017.

A farkon watan nan ne Trump ya sanya harajin kashi 25 cikin 100 kan kayakin akalla dala biliyan 34 da suka kunshi Motoci da kayayakin fasaha mallakin China da ta ke shigarwa Amurkan, matakin da ya kara rura wutar rikicin kasuwancin da ke tsakanin kasashen biyu.

Sai dai tuni shi ma shugaba Xi Jinping na China ya mayar da martani ta hanyar kakaba sabbin haraji kan kayan Amurkan da ke shiga kasar sa.

China ta zargi Amurka da tayar da gagarumin yakin kasuwanci mai cike da tarihin ga tattalin arzikin kasashen duniya.

Cikin cikakakiyar zantawar da aka yi da Trump a yau ya jaddada ikirarin da ya yi na sanya karin haraji kan duk wasu kaya da ake shigarwa kasar daga nahiyar Asiya dama kasashen Turai, yana mai cewa lokaci ya yi da za su kawo karshen ci da gumin Amurka da ake yi a fannin kasuwanci.

Rikicin kasuwancin tsakanin kasashen biyu masu karfin kasuwanci shi ne mafi muni da aka taba gani a tarihi wanda kuma ya sha gaban duk wani rikicin kasuwanci da Donald Trump ya tono bayan hawansa kujerar mulkin kasar bara waccan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.