Isa ga babban shafi
Yemen

Rundunar Saudiya ta kashe kananan yara a Yemen

Akalla kananan yara 29 sun rasa rayukansu a wani hari da rundunar hadaka da Saudiya ke jagoranta ta kaddamar kan motar safa da ke dauke da yaran a yankin arewacin Yemen da ke karkashin ikon ‘yan tawaye.

Jama'a na tururuwa a asibitin da aka kai gawarwakin yaran da aka kashe a harin na Yemen
Jama'a na tururuwa a asibitin da aka kai gawarwakin yaran da aka kashe a harin na Yemen REUTERS/Naif Rahma
Talla

Kungiyar bada agajin ta Red Cross ta ce, jami’anta da ke aikin agaji a wani asibi a kasar sun karbi gawarwakin kananan yara 29 masu kasa da shekaru 15.

Red Cross ta ce, akwai mutane 48 da suka hada da kananan yara 30 da suka jikkata sakamakon kazamin harin na ranar Alhamis.

Rundunar hadakar ta Saudiya ta hakikance cewa, ta kai farmakin ne akan ka'ida don fatattakar ‘yan tawayen Huthi da ke samun goyon bayan kasar Iran.

Kawo yanzu ba a kammala tantance adadin daukacin mutanen da suka rasa rayukansu a harin na kan-mai-uwa-da-wabi ba, amma an tabbatar da alkaluman yaran da suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.