Isa ga babban shafi
Turkiya

Turkiya ta gana da 'yan kasuwa a sassan duniya

Ministan Kudin  Turkiyya ya jagoranci tattaunawa ta hoton bidiyo tsakaninsa da ‘yan kasuwa da masu saka jari sama da dubu uku daga sassa daban daban na duniya, a yunkurin kwantar masu da hankula biyo bayan faduwar darajar kudin kasar saboda takunkuman Amurka.

Darajar kudin Lira na Turkiya na ci gaba da faduwa saboda takunkuman Amurka
Darajar kudin Lira na Turkiya na ci gaba da faduwa saboda takunkuman Amurka REUTERS/Murad Sezer
Talla

Minista Berat Albayrak, ya yi wannan tattaunawa ce tsakaninsa da ‘yan kasuwa da masu saka jari daga kasashen Amurka, Turai da kuma Asiya, wadanda ga alama sun girgiza matuka sakamakon halin da tattalin arzikin kasar ya fada sakamakon takunkuman na Amurka.

Wannan na kara nuni da tasirin ministan wanda ke aure da ‘yar shugaba Erdogan, tare da nuna wa duniya cewa yana da kwarewa da kuma masaniya kan yadda zai iya kwantar da hankulan abokan huldar kasar a fagen tattalin arziki, yayin da alkaluma ke nuni da cewa a tsawon kwanaki uku a jere, takardar kudin Lira na ci gaba da farfadowa.

Minista Abayrak, ya ce ko da wasa, Turkiyya ba za ta nemi taimakon asusun lamuni na duniya domin warware wannan matsala ba, yana mai jaddada wa ‘yan kasuwar cewa, kasar na kan daukar dukkanin matakan da suka wajaba domin tsayawa a kan dugaduganta.

Tuni Turkiyya ta fara daukar matakan ramuwar gayya ta hanyar lafta haraja akan hajojin da ake shiga da su kasar daga Amurka, yayin da ta haramta shigar da wasu a cikin kasar, yayin da a hannu daya Qatar ta sanar da saka jarin Dala milyan dubu 15 don ceto tattalin arzikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.