Obama ya bukaci Amurkawa su juya wa Trump baya
Tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya yi dirar mikiya a kan shugaban kasar mai-ci Donald Trump, inda ya bukaci magoya bayan jam’iyyar Democrat da kuma Republican su nuna rashin amincewa da kamun lodayin shugaban.
Wallafawa ranar:
Tsohon shugaba Obama, a yau asabar zai gudanar da wani gangamin siyasa a jihar California a daidai lokacin da Amurkawa ke shirye-shirye kada kuri’ar tsakiyar wa’adin shugabanci da za a yi cikin watan nuwamba mai zuwa.
Trump dai na shan suka a fannoni da dama, inda hatta a cikin fadarsa wasu bayyana shi a matsayin wanda ba ya da dadin mu’ammala, sannan kuma ba ya mutunta na tare da shi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu