Lula, dake kurkuku ya janye daga takarar shugabncin Brazil
TSOHON Shugaban kasar Brazil Inacio Lula da Silva dake daure a gidan yari, ya janye shirin takarar san a sake neman shugabancin kasar kamar yadda hukumar zabe da kotu ta bada umurni, inda aka maye gurbin sa da mataimakin sa, Fernando haddad.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Wani taron shugabannin Jam’iyyar ma’aikatar kasar da aka gudanar a birnin Curitiba ya amince da sauya dan takarar kafin wa’adin da hukumar zabe gindaya ya cika.
Daruruwan magoya bayan sa suka taru a kofar gidan yarin da ake tsare da tsohon shugaban, yayin da mataimakin nasa ya karanta wasikar da Lula ya rubuta wadda ke tabbatar da shi a matsayin dan takara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu