Isa ga babban shafi
Faransa- Amurka

Shugaban Faransa ya yi kira zuwa Duniya dangane da siyasar Amurka

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya bukaci shugabannin kasashen duniya da suyi watsi da matsayin shugaban Amurka Donald Trump wanda ke ta bayyana kasar sa a matsayin wadda tafi kowacce karfi a duniya, kuma tana iya yin gaban kan ta domin fuskantar duk wani kalubale.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron a zauren majalisar Dinkin Duniya
Shugaban Faransa Emmanuel Macron a zauren majalisar Dinkin Duniya REUTERS/Shannon Stapleton
Talla

Macron wanda bai furta sunan Trump ba a jawabin nasa a zauren Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana manufofi da dama da suka yi karo da na Amurka da suka hada da yarjejeniyar nukiliyar Iran da hulda da kasar, da rikicin gabas ta tsakiya da ya zargi Trump da zafafa shi wajen amincewa da birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra’ila da matsalar talauci a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.