Isa ga babban shafi

Mun hallaka 'yan tawayen Syria dubu 80 - Rasha

Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce akalla ‘yan tawayen Syria dubu 88 ne suka mutu cikin shekaru 3 tun bayan da Moscow ta fara mara baya ga Bashar Al assad wajen ganin ya dawo da karfin ikon da ya ke da shi a kasar, bayan barkewar yaki.

Shoigu wanda ke sanar da adadin yayin taron da ya ke halarta yanzu haka a Singapore ya ce Rasha ta taka muhimmiyar rawa wajen ragargazar 'yan tawayen Syria.
Shoigu wanda ke sanar da adadin yayin taron da ya ke halarta yanzu haka a Singapore ya ce Rasha ta taka muhimmiyar rawa wajen ragargazar 'yan tawayen Syria. Sputnik/Alexei Nikolsky/Kremlin via REUTERS
Talla

Acewar ministan tsaron Rasha fiye da ‘yan tawaye dubu 87 da 500 an ga bayansu ne a hare-haren da aka kai musu, sai kuma wasu dubu 1 da 411 aka kame su yayinda kashi 95 na kasar yanzu haka ya dawo karkashin ikon gwamnatin Bashar Al assad da taimakon Moscow.

Ministan tsaron na Rasha Shoigu, ya ce Rasha ta taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa Bashar al-Assad dawo da karfin iko da ya ke da shi a kasar tare da ragargazar 'yan tawaye.

Sai dai kungiyar kare hakkin dan adam mai sanya idanu kan rikicin na Syria, ta ce kusan mutane dubu 360 ne suka rasa rayukansu a rikicin na Syria cikin shekaru 7 da aka shafe ana yi galibi yayin luguden wutar Rasha a sassan kasar daban-daban.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.