Isa ga babban shafi
Turkiya-Saudiya

Yarima bin Salman ya sha alwashin tabbatar da adalci a kisan Khashoggi

Yarima mai jiran gado na Saudiya Muhammad bin Salman ya sha alwashin gudanar da bincike tare da hukunta dukkanin wadanda ke da hannu a kisan fitaccen dan jaridar kasar mazaunin Turkiya Jamal Kashoggi.

Duk da Amincewarta cewa da hannu wasu 'yan kasar a kisan fitaccen dan jaridar kawo yanzu Saudiya ta gaza bayyana inda gawar Khashoggi ta ke.
Duk da Amincewarta cewa da hannu wasu 'yan kasar a kisan fitaccen dan jaridar kawo yanzu Saudiya ta gaza bayyana inda gawar Khashoggi ta ke. Saudi Press Agency/Handout via REUTERS
Talla

A cewar Yarima Muhammad kisan dan jaridan babban abin takaici ne ga ilahirin al’ummar Saudiya kuma a shirye su ke su hada hannu da hukumomin Turkiya wajen gudanar da bincike tare da bankado wadanda ke da hannu a kisan baya ga hukunta su.

Muhammad bin Salman wanda ke wannan batu kwana guda bayan bude taron kasuwancin kasa da kasa da Saudi Arabia ke karbar bakonci, ya ce duk wani bil’adama dole zai yi alhinin kisan don haka dole ne su hukunta wadanda ke da hannu ciki.

Da farko dai Saudin ta ki amince da zargin cewa da hannunta a kisan fitaccen dan jaridar yayinda daga bisani ta amince amma ta bayyana cewa dan jaridar yayi tsatsatawa ne da juami’an Ofishin jakadancinta da ke birnin na Santambul.

Ka zalika daga bisani Saudin ta fitar da wasu bayanai da ke nuna cewa jami’an Ofishin na ta sun yi kokarin sace Kashoggi ne don mayar da shi kasarshi ta haihuwa amma kuma ya mutu bisa kuskure.

Sai dai kawo yanzu da ilahirin Duniya ta amince da kisan fitaccen dan jaridar wanda ya yi kaurin suna wajen caccakar gidan sarautar Saudiya, Riyadh ta gaza bayyana inda gawar dan jaridar ta ke.

Cikin kalaman da ya gabatar, Muhammad Bin Salman ya ce zuzuta batun kisan dan jaridar da wasu ke yi ba komi ba ne face yunkurin haddasa rikici tsakanin Saudi Arabia da Turkiya wanda ya ce kuma baza su yi nasara ba matukar Saudin na da sarki Salman da kuma yarima mai jiran gado Muhammad.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.