Isa ga babban shafi
Yemen-Houthi

Harin Sojin hadaka ya hallaka 'yan tawayen Houthi 58 a Yemen

Akalla ‘yan tawayen Houthi 58 ne suka mutu yayin wata fafatawa hade da hare-hare ta sama da Sojin hadakar kasashen larabawa karkashin jagorancin Saudiya mai mara baya ga gwamnatin Yemen ta kai kan ‘yan tawayen a birnin Hodeida yau Alhamis.Hare-haren dai na zuwa a dai dai lokacin da kungiyoyin agaji ke ci gaba da gargadin tsanantar yunwa a kasar ta Yemen.

kungiyoyin agajin sun yi gargadin cewa akwai karin akalla mutane miliyan 14 da za su fada cikin matsananciyar yunwa a kasar sakamakon yakin na Hodeida.
kungiyoyin agajin sun yi gargadin cewa akwai karin akalla mutane miliyan 14 da za su fada cikin matsananciyar yunwa a kasar sakamakon yakin na Hodeida. AFP
Talla

Wata majiyar asibiti a birnin na Hodeida mai arzikin ruwa, ta shida cewa cikin dare hare-haren sojin hadakar ya hallaka ‘yan tawayen 47, yayinda zuwa safiyar yau aka kara hallaka wasu 11.

Yaki tsakanin ‘yan tawayen na Houthi da yanzu haka ke rike da wani bangare na Hodeidar na kara rincabewa ne bayan matakin dakarun hadakar na ganin sun kwace iko da ilahirin birnin dama sauran sassan kasar ta Yemen.

Sai dai kuma matakin na zuwa ne a dai dai lokacin da kungiyoyin agaji ke ci gaba da kururuwar gargadi game da halin matsananciyar yunwar da al’ummar kasar za su kara tsunduma sanadiyyar yakin na Hodeida la’akari da yadda birnin ke matsayin zuciyar kasuwancin kasar.

Ka zalika, kungiyoyin agajin sun yi gargadin cewa akwai karin akalla mutane miliyan 14 da za su fada cikin matsananciyar yunwa a kasar sakamakon yakin na Hodeida.

A bangare guda kuma kungiyar Amnesty International ta nuna fargaba kan yadda ‘yan tawayen na Houthi yanzu haka suka fara amfani da asibitoci a matsayin mafaka, inda ta ce akwai tsoron kada hare-haren sojin hadakar ya shafi marasa lafiyar da ke kwance a asibiti da ma likitocin da ke duba lafiyarsu.

A cewar kungiyar duk da matakin na Houthi ya sabawa dokokin kare hakkin bil’adama dama duk wata dokar yakin kasa da kasa, amma hakan baya nufin cewa kai tsaye dakarun hadakar za su kai hare-hare kan asibitocin don yin hakan na matsayin mafi munin take hakkin bil’adama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.