Isa ga babban shafi
Isra'ila

Makomar Netanyahu na cikin tsaka mai wuya

Makomar Gwamnatin Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu na cikin tsaka mai wuya bayan Ministan Tsaronsa, Avigdor Lieberman ya yi murabus daga mukaminsa sakamakon yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma tsakanin Isra’ila da Falasdinawa.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu REUTERS/Amir Cohen
Talla

Lieberman ya yi murabus ne daga kujerasa don nuna rashin jin dadinsa da matakin da gwamnatin Netanyahu ta dauka na amincewa da yarjejeniyar kawo karshen rikicin kwanaki biyu da ya lakume rayukan Falasdinawa a Gaza, abin da ya bayyana a matsayin mika wuya ga ta’addanci.

Ana ganin murabus dinsa na da tasirin da ka iya yin tarnaki ga makomar Netanyahu, lura da cewa, ya dauki matakin ne a yayin da ake shirin gudanar da zaben gama-gari a watan Nuwamban badi duk da cewa, watakila a maso da lokacin zaben baya.

Mitchelle Barack, mashawarcin tsohon shugaban Isra’ila, Shimon Perez, ya ce, “matakin murabus din Lieberman a wannan lokacin ya yi daidai, domin kuwa da ya haifar da tarnaki ga zaben da za a gudanar.”

“Tabbas ya sanar da mu cewa, zai yi murabus daga wannan gwamnati, amma ina ganin akwai wata manufa ta siyasa da yake fatan cimma. Yanzu haka, ya rage ga Firaminista da ya yi kurda-kurdar nema wa kansa mafita saboda har yanzu yana da tacewa.” In ji Barack.

Mai magana da yawun rundunar Falasdinawa ta musamman Nour Odeh ta ce, murabus din Liebermann ba shi da wani tasiri a kansu.

“Ina ganin daukacin al’ummar Falasdinu ba za su rasa wani abu ba saboda ficewar Liebarman daga wannan gwamnatin, kuma ya yi murabus ne saboda adawa da kawo karshen zubar da jinin Falasdinawa. Murabus dinsa ba zai sauya matsayar Israila ba, amma watakila murabus din ya sauya salon siyasar kasar.” In ji Odeh.

Yanzu haka, Liebermann zai yi awon gaba da kujeru biyar da jam’iyyarsa ke da su a Majalisar Dokokin Isra’ila kuma a karkashin gamayyar jam’iyyun da gwamnatin Netanyahu ke jagoranci.

Kungiyar Hamas da aminiyarta ta Islamic Jihad ta yi farin ciki matuka da murabus din Lieberman, abin da suka bayyana a matsayin nasara a gare su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.