Isa ga babban shafi
Isra'ila

Ministan Tsaron Isra'ila ya yi murabus

Yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma tsakannin gwamnatin Isra'ila da kungiyoyin gwagwarmayar Falesdinawa dake dauke da makamai Hamas da Jihad Islamiya ta haifar da rarrabuwar kanu a cikin gwamnatin Isra'ila da ya haifar da murabus din Min istan tsaron kasar Avigdor Lieberman.

Avigdor Lieberman, Tsohon Ministan tsaron Isra'ila
Avigdor Lieberman, Tsohon Ministan tsaron Isra'ila REUTERS/Amir Cohen
Talla

Avigdor Lieberman tsohon  ministan tsaron Isra'ila a wata ganawa da manema labarai ya bayyana cewa shiga tattaunawa da kungiyoyin falesdinawa ya sabawa manufofin jam'iyyar sa,tattaunawar na a matsayin mika wuya.

Ficewar Ministan tsaron Isra’ila na nuna rarrabuwar kawuna da gwamnatin kasar ke fuskanta yanzu haka tun bayan da yan kungiyar Hamas suka harba makaman roka 460 cikin kasar. Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar da taro a asirce amma babu wani bayani da akayi a kai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.