Isa ga babban shafi
Iran-Birtaniya

Sakataren wajen Birtaniya na ziyara a Iran kan shirinta na Nukiliya

Sakataren wajen kasar Birtaniya Jeremy Hunt ya isa birnin Tehran domin ganawa da mahukuntan kasar Iran dangane da shirin nukiliyar kasar, da kuma kokarin ganin Iran ta saki wasu ‘yan Birtaniya da ke tsare a gidajen yarin kasar.

Takunkuman da Amurkan ta mayar kan Iran da suka fara aiki ranar 5 ga watan Nuwamban nan kai tsaye sun haramtawa kasashen duniya sayen man Iran wanda ke da nufin tagayyara tattalin arzikin kasar.
Takunkuman da Amurkan ta mayar kan Iran da suka fara aiki ranar 5 ga watan Nuwamban nan kai tsaye sun haramtawa kasashen duniya sayen man Iran wanda ke da nufin tagayyara tattalin arzikin kasar. HO / Iranian Presidency / AFP
Talla

Tuni sakataren wajen na Birtaniya ya gana da takwaransa na Iran Mohammad Javad Zarif, a wannan ziyara ta farko da ministan ya kai tun lokacin da Amurka ta janye daga yarjejeniyar nukiliyar Iran a watan mayun da ya wuce.

Tun a bara ne Amurka ta sanar da ficewa daga yarjejeniyar nukiliyar Iran yarjejeniyar da ta bai wa kasar damar hulda da manyan kasashen duniya musamman ta fuskar kasuwanci da bunkasa tattalin arziki.

Sai dai tun bayan ficewarta manyan kasashe da kamfanoni ke ci gaba da janyewa daga hulda da kasar yayinda Amurkan ta mayar da dukkanin takunkuman da a baya aka sanya wa Iran musamman na baya-bayan nan da kai tsaye ya shafi cinikayyarta ta man fetur ko da dai Amurkan ta zabe wasu kasashe 8 da ta ce takunkuman ba zai shafe su ba ko da sun yi kasuwanci da Iran. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.