Isa ga babban shafi
Amurka

Kotu ta dakatar da Trump kan hana baki mafaka

Wani alkalin kotun tarayya a Amurka ya dakatar da umarnin shugaba Donald Trump na hana bada mafaka ga baki ‘yan gudun hijira da ke shiga cikin kasar ba bisa ka’ida ba ta kan iyakar yankin kudancin kasar.

Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar da suka doshi Amurka ta kan iyakar Mexico
Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar da suka doshi Amurka ta kan iyakar Mexico REUTERS/Ueslei Marcelino
Talla

Alkalin kotun da ke San Fransisco, Jon Tigar ya dauki matakin ne bayan sauraren korafin da wasu kungiyoyin fararen hula suka shigar.

A farkon wannan watan ne shugaba Trump ya sanya hannu kan takardar umarni don dakile ayarin ‘yan gudun hijirar da ya doshi Amurka.

Trump ya ce, akwai bukatar daukan matakin saboda kare manufofin Amurka, amma kungiyoyin farraen hula suka nuna adawa da shi daga Honduras da Guatemala da kuma El Salvador.

A yayin yanke hukuncin, alkalin kotun ya ce, dokokin da ake amfani da su a yanzu, sun bai wa duk wani bako da ke shiga Amurka ta kowacce hanya damar neman izinin fakewa a kasar.

A cewar Alkalin, shugaba Trump ba zai sake rubuta dokar shige da fice ta kasar ba duk kuwa da karfin ikonsa ba tare da amincewar Majalisar Dokoki ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.