Trump ya yi barazanar soke ganawa da Putin
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar soke ganawar da ya tsara yi da shugaban Rasha Vladimir Putin a gefen taron kasashe 20 masu karfin tattalin arziki a duniya da zai gudana a birnin Buones Aires na kasar Argentina a karshen wannan mako.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Ukraine Petro Poroshenko ya sanya hannu kan dokar ta baci a lardunan da ke kan iyakar kasar da Rasha, sakamakon kama jirgin ruwan da dakarun Rasha suka yi a mashigin ruwan Azov.
Kafa dokar ta bacin har tsawon kwanaki 30 masu zuwa, wata alama ce da ke kara tabbatar da cewa alaka ta yi tsami sosai tsakanin Rasha da makociyarta Ukraine, wadanda suka jima suna takun-saka tun bayan ballewar yankin Cremea.
Da farko dai an tsara ganawa tsakanin Donald Trump ta Vladimir Putin a gefen taron kasashen duniya 20 masu karfin tattalin arziki wato G20 a birnin Buenos Aires karshen wannan mako, to sai dai Trump ya yi barazanar soke ganawar.
Shugaba Putin a wannan laraba, ya ce matakin da dakarun kasar suka dauka na cafke jirgin ruwan kasar ta Ukraine ba inda ya saba wa doka, kuma yanzu haka mutane 24 da aka kama a wannan jrgi na cigaba da kasancewa a hannun mahukuntan kasar Rasha.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu