Isa ga babban shafi
Amurka-Rasha

Amurka da Rasha na ganawa kan yarjejeniyar kayyade muggan makamai

Jakadun Diflomasiyyar kasashen Rasha da Amurka za su yi wata ganawa ta musamman kowanne lokaci a yau Talata don tattaunawa game da barazanar Amurka na ficewa daga yarjejeniyar kayyade adadin muggan makamai da kasashen biyu ke kerawa wadda suka cimma tsawon shekaru bayan da Washington ta yi zargin cewa Moscow na yi wa yarjejeniyar karantsaye.

Watanni biyu da suka gabata ne Donald Trump na Amurka ya fara barazanar juyawa yarjejeniyar baya wadda aka cimma tun a shekarar 1987 bayan kawo karshen yakin cacar baka.
Watanni biyu da suka gabata ne Donald Trump na Amurka ya fara barazanar juyawa yarjejeniyar baya wadda aka cimma tun a shekarar 1987 bayan kawo karshen yakin cacar baka. REUTERS/Leonhard Foeger
Talla

Tattaunawar wadda za ta gudana a Geneva, ana sa ran ta kawo karshen fargabar da ake ta warwarewar yarjejeniyar wadda za ta iya haddasa yawaita da kuma kwararar muggan makamai a sassan duniya.

A cewar Andrea Thompson sakatariyar sashen kula da manyan makamai ta Amurka wadda ke jagorancin tawagar kasar a tattaunawar, ta ce Rashan ta kera wasu muggan makamai da suka tsallake dokokin da yarjejeniyar ta gindaya.

Andrea Thompson ta ce yayin tattaunawar suna fatan janyo hankalin Rasha don dawowa cikin yarjejeniyar baya ga dakatar da ayyukan kera wasu manyan makamai da ta yi wanda ke barazanar ga dorewar yarjejeniyar da aka cimma a shekarar 1987 tsakanin tsohon shugaban Amurkan Ronald Reagan da na Rashan Mikhail Gorbachev.

Sai dai a bangaren Rashan babu jami’I guda da ya yi jawabi ga manema labarai dai dai lokacin da ake shirin fara tattaunawar a wani ginin Diflomasiyyar Rashan da ke birnin na Geneva.

Ko a watan jiya sai da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya bayar da wa’adin kwanaki 60 kan cewa ko dai Rasha ta kunce dukkannin makaman da ta kera ko kuma Amurkan ta fice daga Yarjejeniyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.