Isa ga babban shafi
Birtaniya-EU

Ga alama Birtaniya za ta yi baran-baran da EU

Kungiyar Tarayyar Turai da ma sauran kasashe mambobinta, sun ce lura da kuri’ar da ‘yan majalisar Birtaniya suka kada da ke yin watsi da yarjejeniyar da Theresa May ta kulla da kungiyar, akwai yiyuwar za a raba gari tsakanin bangarorin biyu ne ba tare da wata jituwa ba.

Firaministar Birtaniya Theresa May na fuskantar tirjiya daga 'yan majalisar kasarta dangane da amincewa da yarjejeniyar ficewa daga Kungiyar Tarayyar Turai
Firaministar Birtaniya Theresa May na fuskantar tirjiya daga 'yan majalisar kasarta dangane da amincewa da yarjejeniyar ficewa daga Kungiyar Tarayyar Turai REUTERS
Talla

Jagoran tawagar Turai a tattaunawar Michel Barnier da kuma shugaban Hukumar Tarayyar Turan Jean-Claude Juncker, sun ce sakamakon kuri’ar da aka kada a ranar Talata, na kara tabbatar da cewa abu ne mai yiyuwa a kai 29 ga watan Maris wa’adi na karshe ba tare da wata yarjejeniya tsakaninsu da Birtaniya ba.

Ministan Kudin Jamus kuwa Olaf Scholz, ya bayyana kayen da Theresa May ta sha cikin zauren majalisar a ranar Talata da cewa babban abin taikaici ne.

To sai dai shugaban Faransa Emmanuel Macron, shawara ya bayar cewa, kamata ya yi bangarorin biyu su fara tattaunawa domin tsawaita wa’adin ficewar kasar ta Birtaniya, yana mai cewa ko shakka babu, ‘yan Birtaniya ba za su yi fatan ganin jiragensu sun daina tashi daga Turai ba, tare da hana su yin cinakayyar da za ta kai kashi 70% da ‘yan uwansu na yankin Turai ba.

A nasa bangare kuwa Firaministan Austria Sebastian Kurz cewa ya yi, sam ba za a zauna da Birtaniya don sake bitar yarjejeniyar da aka kulla a baya ba, yayin da takwaransa na Spain Pedro Sanchez ya ce, isa wancan lokaci ba tare da an cimma wata matsaya ba, lamari ne da zai shafi kowanne daga cikin bangarorin biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.