Isa ga babban shafi
Amurka-Mexico

Trump ya dora alhakin kulle ma'aikatun kasar kan 'Yan Democrats

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sha alwashin ci gaba da kulle ma’aikatun kasar har zuwa lokacin da majalisa za ta sahale masa sama da dala biliyan 5 don gina katanga akan iyakar kasar da Mexico dai dai lokacin da ma’aikatun ke shiga kwana na 32 a kulle.

Sakon na Trump wanda ke zuwa dai dai lokacin da ma'aikatun kasar ke cika kwanaki 32 a kulle ya ce 'yan Jam'iyyar Democrats ne ke da alhakin iya kawo karshen kulle ma'aikatun.
Sakon na Trump wanda ke zuwa dai dai lokacin da ma'aikatun kasar ke cika kwanaki 32 a kulle ya ce 'yan Jam'iyyar Democrats ne ke da alhakin iya kawo karshen kulle ma'aikatun. ©REUTERS/Yuri Gripas
Talla

Cikin sakon Twitter da ya wallafa Donald Trump kai tsaye ya dora laifin ci gaba da kasancewar ma’aikatun kasar a kulle kan ‘yan majalisun Jam’iyyar Democract ya na mai cewa har sai sun amince da ware masa dala biliyan 5 da miliyan 700 don gina katanga a iyakar kasar da Mexico ne tukuna zai sahale fitar da kudaden tafiyar da ma’aikatun don kawo karshen kasancewarsu a kulle.

A cewar Trump matukar ba a gina katangar ba, hakan na nuna cewa Amurka ba ta da iyaka haka zalika ba za ta iya samarwa al’ummarta cikakken tsaro ba, wanda ya ce Democract ta san hakan kawai ta na sanya bukatunta na siyasa a gaba ne maimakon amfanuwar al’ummarta.

Matakin kulle ma’aikatun cikin har da FBI na da nufin tirsasa ‘yan majalisun Jam’iyyar Democract masu rinjaye a majalisa amincewa da kudirinsa na samar da kudaden ginin katangar, sai dai shugabar majalisar Nancy Pelosi ta yi watsi da bukatar da Trump tun kafin zuwanta gaban Majalisa, dama bayan bayyanar kudirin gabanta.

Pelosi a na ta sakon ta shafin Twitter da ke matsayin mayar da martini ga kalaman Trump, ta ce kai tsaye Trump ya kamata a zarga ta na mai cewa ya gaggauta kawo karshen kulle ma’aikatun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.