Isa ga babban shafi
VENEZUELA

Kwamitin Sulhu zai gana kan rikicin Venezuela

Amurka ta bukaci Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya gudanar da wani zama na musamman domin tattaunawa kan rikicin siyasar Venezuela. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Majalisar Sojin Kolin Kasar ta nuna goyon bayanta ga shugaba Nicolas Maduro, yayin da ta zargi jagoran ‘yan adawa Juan Guaido da yunkurin juyin mulki.

Shugaban Venezuela, Nicolás Maduro
Shugaban Venezuela, Nicolás Maduro Miraflores Palace/Handout via REUTERS
Talla

Amurka da sauran aminanta a yankin Latin na mara baya ga jagoran ‘yan adawar ta Venezuela, Juan Guaido da ke bayyana kansa a matsayin mukaddashin shugaban kasa, yayin da Amurkan ke cewa, gwamnatin Maduro ba halastacciya bace.

Mike Pompeo  Sakataren Harkokin Wajen Amurka, ya ce, “A matssayinmu na aminan al’ummar Venezuela, za mu ci gaba da taimaka masu, domin ganin cewa sun gina kasa da kuma tattalin arzikinsu da ya ruguje sakamakon jagorancin dan kama-karya, bami wanda kuma ba ya da halasci."

Sai dai majalisar manyan Janar-Janar da ke kula da muhimman wurare a Venezuela ta jaddada goyon bayanta ga Maduro wanda ta ce, mai gaskiya ne a koda yaushe kuma ba maci amanar kasa ba ne.

A gefe guda, Rasha da China da Mexico da Cuba da Bolivia na goyon bayan Maduro ne, yayin da Faransa da Canada ke mara wa jagoran ‘yan adawar kasar, wato Juan Guaido.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.