Isa ga babban shafi
Venezuela-Maduro

'Yan Venezuela na gangamin adawa da Maduro bayan dawowar Guaido

Dubun dubatar al’ummar Venezuela da ke mara baya ga bangaren adawa sun fara gagarumar zanga-zanga bisa bukatar madugun adawa Juan Guaido, wanda ya koma kasar yau daga ziyarar neman goyon bayan da ya yi a kasashen latin Amurka.

Yanzu haka dai Guaido ya isa birnin Caracas inda ya ke jagorantar gangamin adawa da shugaba Nicolas Maduro ba kuma tare gwamnati ta hukunta shi ba
Yanzu haka dai Guaido ya isa birnin Caracas inda ya ke jagorantar gangamin adawa da shugaba Nicolas Maduro ba kuma tare gwamnati ta hukunta shi ba REUTERS/Luisa Gonzalez
Talla

Jagoran adawar na Venezuela Juan Guaido wanda ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa na rikon kwarya, a yammacin yau ne ya dawo Venezuelan baya da ya bukaci gangamin a sassan kasar don kara tirsasawa Nicolas Maduro sauka daga mulki.

Sai dai dawowar ta Juan Guido daga ziytarar kasashen Latin Amurka, masu mara masa baya, na cike da shakkun yiwuwar kame shi daga bangaren gwamnati, wadda ta haramta masa fita daga kasar amma ya silale a makon jiya, ko da dai tuni kasar Amurka ta yi gargadi kan abin da zai biyo baya, matukar aka kame jagoran adawar.

Tun a jiya Lahadi ne Guaido wanda ke samun goyon bayan kasashen duniya 50, ya umarci masu mara masa baya a cikin kasar ta Venezuela su fito gangamin da misalin karfe 11 na safiyar agogon kasar.

A ranar 23 ga watan jiya ne, Guaido mai shekaru 35 wanda ke fuskantar haramci fita daga Venezuela ya silale ta hanyar bin wasu manyan motoci zuwa iyakar kasar da Colombia inda daga nan ne ya samu ganawa da mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence.

Yanzu haka dai Guaido ya isa birnin Caracas inda ya ke jagorantar gangamin adawa da shugaba Nicolas Maduro ba kuma tare gwamnati ta hukunta shi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.