Isa ga babban shafi
New Zealand

Firaministar New Zealand ta bukaci kawar da wariya a duniya

Firaministar New Zealand, Jacinda Ardern ta bukaci kasashen duniya da su tashi tsaye wajen yaki da kawar da akidar wariyar launin fata bayan harin ta’addancin da ya kashe mutane 50 a wasu Masallatai biyu da ke birnin Christchurch a makon jiya.

Firaministar New Zealand  Jacinda Ardern ta ziyarci al'ummar Musulmi bayan harin Masallatai biyu a Christchurch
Firaministar New Zealand Jacinda Ardern ta ziyarci al'ummar Musulmi bayan harin Masallatai biyu a Christchurch New Zealand Prime Minister's Office/Handout via REUTERS
Talla

A yayin tattaunawa da manema labarai, Ardern ta yi watsi da batun cewa, kwararar ‘yan gudun hijira ne ke rura matsalar wariyra launin fata.

Tuni aka fara gudanar da jana’izar Musulman da aka kashe a harin na bindiga, in da a yau Laraba aka binne wani magidanci dan asalin Syria da kuma dansa da suka rasa rayukansu a mummunan farmakin.

Daruruwan jama’a sun halarci jana’izar wadda aka gudanar a makabartar Linwood ta Musulmai da ke birnin na Christchurch.

Kotu ta tuhumi Brenton Tarrant, dan asalin kasar Australia mai shekaru 28 da laifin kisa a harin da ya kaddamar kan Musulman a ranar Jumma’ar da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.