An yi Jana'izar wadanda suka mutu a harin Masallacin New Zealand
Yau an gudanar da jana’izar wasu daga cikin mutane da wani dan bindigar ya harbe a Masallatan juma’ar kasar makon jiya, yayin da Firaministar kasar Jacinda Ardern ta bukaci kasashen duniya su hada kai domin daukar mataki kan kafofin sadarwar da ke baiwa masu tsattsauran ra’ayi damar yada manufofin su.
Wallafawa ranar:
Daruruwan mutane da suka hada da Musulmi da ma wadanda ba Musulmi ba ne suka halarci jana’izar a wata makabarta da ke kusa da Masallachin Linwood, daya daga cikin Masallatan da aka kai harin.
Firaminista Jacinda Ardern ta ce ya zama wajibi duniya ta dauki mataki kan kafofin sada zumunta.
A juma'ar da ta gabata ne dai, wani dan bidiga ya bude wuta kan mabiya addinin Islama da ke halartar sallar Juma'a tare da hallaka mutane 49.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu