Isa ga babban shafi
New Zealand

Maharin New Zealand na da alaka da kungiyar Austria

Shugaban Gwamnatin Austria, Sebastian Kurz ya bayyana cewa, mutumin da ya kashe Musulmai 50 a Masallatan New Zealand, ya bada taimakon kudi ga kungiyar da ke rajin fifita farar fata ta Austria.

Brenton Tarrant dan bindigar da ya hallaka Masallata 50 a wasu Masallatan Juma'a 2 da ke New Zealand, a tsakiyar jami'an tsaro.
Brenton Tarrant dan bindigar da ya hallaka Masallata 50 a wasu Masallatan Juma'a 2 da ke New Zealand, a tsakiyar jami'an tsaro. Mark Mitchell/New Zealand Herald/Pool/REUTERS.
Talla

Shugaban Gwamnatin Austria, Sebastian Kurz ya bayyana cewa, akwai alaka tsakanin wannan maharin da kuma Kungiyar Rajin Fifita Farar Fatar ta Austrian.

Mai magana da yawan masu shigar da kara a birnin Graz da ke kudancin Austria, ya ce, shugaban kungiyar, Martin Sellner ya karbi Euro dubu 1 da 500 a matsayin tallafi daga hannun wani mutun da sunansa ya yi daidai da na maharin na Masallatan birnin Christchurch a New Zealand.

Shugaban Kungiyar ta Masu Rajin Fifita Farar Fatar, ya wallafa hoton bidiyo a YouTube, in da yake cewa tabbas, ya karbi kudin tallafi dauke da sakon email da ke tattare da suna irin na wannan mahari.

Kudin da ya ce, ya karbe shi a shekarar 2018, yanzu haka zai mika shi ga gidauniyar agaji a cewarsa.

Sellner ya kuma kara da cewa, jami’an ‘yan sanda sun kai samame cikin gidansa bisa zargin alakarsa da maharin na Christchurch.

Jami’an ‘Yan sandan New Zealand sun ce, kwararru na gudanar da bincike mai zurfi a sassan kasar da kuma wasu kasashen duniya duk dai akan batun harin, yayin da Shugaban Gwamnatin na Austria ya ce, a halin yanzu suna duba yiwuwar rusa wannan kungiya a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.