Za a sake gina Venezuela da Dala biliyan 10
Amurka ta ce yanzu haka tana aiki tare da wasu kasashen duniya domin tara dala bilyan 10, wadanda za a yi amfani da su wajen sake gina kasar Venezuala matukar dai aka kafa sabuwar gwamnati a kasar.
Wallafawa ranar:
Sakataren baitul-malin Amurka Steven Mnuchin ne ya sanar da hakan a daidai lokacin da takwaransa na harkokin waje Mike Pompeo ke ganawa da shugabannin kasashen yankin latin Amurka da ke ci gaba da bayyana Juan Guaido a matsayin wanda ke da halascin shugabancin kasar ta Venezuela.
Mnuchin ya ce, Amurka za ta yi iya kokarinta domin ganin cewa an tara wadannan kudade, kuma tuni Asusun Lamuni na Duniya da kuma Bankin Duniya suka amince da wannan shiri don ceto kasar.
To sai dai a cewarsa, Amurka ba za ta amince wadannan cibiyoyi na kudade sun bayar da tallafi ga Venezuela ba har sai zuwa lokacin da aka kafa sabuwar gwamnati da ‘yan kasar suka amince da ita.
Sakataren baitul-malin na Amurka ya ce tabbas jama’ar kasar ta Venezuela na bukatar taimakon gaggawa sakamakon yadda lamurra suka lalace, inda alkaluma ke nuni da cewa adadin ‘yan kasar da suka tsere zuwa ketare saboda rashin iya jagorancin Nicolas Maduro sun kai milyan 3 da dubu 700 a halin yanzu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu