Isa ga babban shafi
MDD- Sauyin Yanayi

MDD ta kaddamar da sabon yunkuri kan sauyin yanayi

Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da sabon yunkurin magance gurbacewar muhalli, matsalar da Sakatare Janar na Majalisar, Antonio Guterres ya bayyana a matsayin babban abinda ke ci wa duniya tuwo a kwarya a wannan zamanin.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres REUTERS/Denis Balibouse/File photo
Talla

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Goterres ya ziyarci kasar New Zealand a karshen mako, inda daga nan zai yi balaguro zuwa kasashen da ke yankin tsibirin Pacific da ke fuskantar barazana shafewa sakamakon tunbatsar tekuna.

A wani muhimmin sako da ya aika, Guterres ya ce, ana samun jan kafa waje tunkarar matasalar sauyin yanayi, yana mai cewa, kasashen da ke yankin tsibirin Pacific na kan gaba wajen fuskantar barazana, kuma su ne za su fi shan wahala.

Guterres zai kuma gana da iyalan mutanen da rayuwarsu ta shiga tsaka mai wuya sakamakon ambaliyar ruwa da guguwa a wadannan kasashe na Pacific.

Wannan yunkurin diflmasiyar da Guterres ya kaddamar, zai kai ga shirya wani taro a cikin watan Satumba a zauren Majalisar Dinkin Duniya, taron da ake kallo a matsayin dama ta karshe ta magance sauyin yanayi a daidai lokacin da aka cika shekaru uku da fara aiwatar da yarjejeniyar birnin Paris.

Sai dai Guterres ya ce, bisa dukkan alamu, har yanzu ba a kama hanyar cimma muradun da aka shata a taron na birnin Paris ba, lura da gazawar kasashen duniya wajen rage gurbacewar muhalli da akalla kashi 1.5 a ma’aunin Celsius.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.