Isa ga babban shafi

Macron ya tattauna da Trump kan rikicin Amurka da Iran

Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta tabbatar da tattaunawar shugaban kasar Donald Trump da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron a yammacin jiya Juma’a, tattaunawar da ta mayar da hankali kan tsamin alakar da ke tsakanin kasar ta Amurka da Iran.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron screenshot Youtube
Talla

Sanarwar White House da ke tabbatar da tattaunawar shugabannin biyu ta wayar tarho, ta ce Faransa ta alkawartawa Amurka ganin cewa Iran ba ta mallaki makamin Nukiliya ba.

Shugaban na Faransa Emmanuel Macron dai, shi ne na gaba-gaba a cikin shugabannin Turai da ke neman shiga tsakani game da rikicin kasashen biyu.

Ka zalika tattaunawar na zuwa ne bayan da Amurka ta sanar da kakkabo jirgin Iran marar matuki a mashigin ruwan Hormuz ko da dai Iran ta musanta batun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.