Isa ga babban shafi

Trump ya zargi Iran da rura rikici bayan kwace tankokin man Birtaniya

Amurka ta zargi Iran da rura wutar rikici tare da takalar fada bayan sanarwar dakarun juyin-Juya halin kasar ta Iran wadda ta yi ikirarin kwace tankokin man Birtaniya.

Shugaban Amurka Donald Trump lokacin da ya ke jawabi kan daukar sabbin matakai kan Iran bayan kwace jiragen ruwan Birtaniya
Shugaban Amurka Donald Trump lokacin da ya ke jawabi kan daukar sabbin matakai kan Iran bayan kwace jiragen ruwan Birtaniya © REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

A jawabansa gaban manema labarai, Donald Trump ya ce ba wai tank ace guda daya ko guda biyu ba, za su iya dara haka, a don haka ya zama wajibi Amurka ta taimakawa Birtaniya.

Donald Trump yayin jawabin nasa ga manema labarai, y ace zai tattaunawa da Birtaniya don sanin ta yadda zai taimaka mata.

Tun a yammacin jiya juma'a ne, jami’an da ke tafe da tankokin man na Iran suka tabbatar da cewa, an kwace iko da jirginsu kuma yanzu haka suna kan hanyar tunkarar Iran.

A bangare guda itama Birtaniya ta tabbatar da kwace mata jiragen har guda 2 a mashigin ruwan Hormuz inda ministan harkokin wajenta Jeremy Hunt, ke cewa kasar ba za su lamunci take-taken na Iran ba.

Cikin sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Birtaniyar ta fitar, ta yi tir da matakin na Iran inda ta ce kwace jiragen babban abin damuwa wanda dole ne ta dauki kwararan matakai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.