Isa ga babban shafi
G7- Brazil

Brazil ta yi watsi da tallafin G7 don kashe gobarar dajin Amazon

Gwamnatin Brazil ta yi watsi da tallafin yuro miliyan 20 da taron kasashe 7 mafiya karfin tattalin arziki ya hada mata don yaki da gobarar dajin Amazon wadda yanzu haka ke ci gaba da banna a sassan kasar, inda sanarwar Brazil ta bukaci shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya yi amfani da kudin don gyara kasarsa.

A tract of the Amazon jungle burns as it is cleared by loggers and farmers in Porto Velho, Brazil August 24, 2019.
A tract of the Amazon jungle burns as it is cleared by loggers and farmers in Porto Velho, Brazil August 24, 2019. REUTERS/Ueslei Marcelino
Talla

Daga farkon shekarar nan kawo yanzu, akalla gobara dubu tamanin ce ta tashi a dazukan kasar Brazil galibi kuma a dajin na Amazon wanda ke samar da kusan kashi 50 cikin dari na isakar da al’ummar duniya ke shaka.

Tun gabanin fara taron G7 da faransa ta karbi bakonci can a birnin Biarritz, shugaba Emmanuel Macron ya nemi taron ya tattauna don yaki da gobarar dajin na Amazon matakin da ya bayarda damar hada kudi yuro miliyan 20 ba ya aikewa da jiragen kashe gobara don kawo karshen gobarar dajin na Amazon wanda yankinsa mai yawa ke cikin kasar Brazil.

Sai dai gwamnati Jair Bolsonaro wadda tun tuni ta yi kakkausar suka kan matakin tare da zargin Macron da yiwa harkokin cikin gidan Brazil Katsalandan, ta ce Emmanuel Macron ke bukatar kudaden amma ba kasar Brazil ba.

Cikin jawaban kai tsaye da shugaban ma’aikatan gwamnatin Bolsanaro, Onxy Lorenzoni ya gabatar ta gidan talabijin din GI ya ce sun yaba da matakin taron na G7 amma zai fi muhimmanci ayi amfani da kudaden wajen samar da ayyuka a nahiyar Turai.

Cikin kalaman Lorenzoni wanda kai tsaye ya ke shagube ga Emmanuel Macron, ya ce mutumin da ya gaza samar da kudin gyaran majami’ar Notre-Dame da gobara ta bannata shi ne ke kururuwar ganin an hada kudi don magance gobarar dajin Amazon.

Kafin yanzu dai ministan muhalli na Brazil Ricardo Salles ya yaba da kokarin na G7 wajen taimaka don kashe gobarar dajin na Amazon da ta lalata kadada kusan miliyan 2 da rabi.

Sai dai bayan wata ganawar gaggawa tsakanin shugaba Bolsanaro da mukarraban gwamnatinsa, shugaban ya yi watsi da tallafin kudaden.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.