Isa ga babban shafi
Afghanistan

An yi kokarin kashe mataimakin shugaban kasar Afghanistan

A kasar Afghanistan, dan kunar bakin wake ya tayar da bam a lokacin da ayarin mataimakin shugaban kasar Amrullah Saleh ke wucewa sanyin safiyar yau laraba a birnin Kabul.

dan kunar bakin wake ya tayar da bam a lokacin da ayarin mataimakin shugaban kasar Amrullah Saleh ke wucewa
dan kunar bakin wake ya tayar da bam a lokacin da ayarin mataimakin shugaban kasar Amrullah Saleh ke wucewa Najiba NOORI / AFP
Talla

Takanas yan kungiyar Hezbollah suka  nisanta kan su daga harin ,kamar dai yada  mai magana da yahun kungiyar  Zabihullah Mujahid ya sheidawa kamfanin dilancin labaren Faransa na AFP.

Shugaban kasar Ashraf Ghani ya dai yi Allah wadai da harin,inda ya bayyana cewa Gwamnati za ta dau matakan da suka dace don yaki da yan ta'adda a kasar.

Mutane shida ne aka bayyana sun mutu,wasu da dama suka samu raunika.

Daya daga cikin manyan jami’an gwamnati da ke cikin ayarin mai suna Razwan Murad, ya ce an nufi mataimakin shugaban ne da wannan hari, to amma yana cikin koshin lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.