Isa ga babban shafi
G20

Saudiya na karbar bakwancin taron G20

Kasar Saudi na karban bakuncin taron kasashe masu karfin tattalin arziki na G20, yau Asabar, taron na hoton bidiyo wanda zaifi daukar hankali kan batun kawo karshen cutar korona da batun rigakafin da aka samar da kuma hanyar farfado da tattalin arziki, shine karo na farko da wata kasar Larabawa zata shirya.

Sarki Salman na Saudiya.
Sarki Salman na Saudiya. Alexander Zemlianichenko/Pool via REUTERS
Talla

Taron na kwanaki biyu, na zuwa ne adai-dai lokacin da Shugaba Donald Trump ya ki amincewa da kayin da ya sha a zaben shugabancin Amurka, yayin da masu fafutuka ke sukar kasashen G20 da abin da suka kira rashin daukar matakan da suka dace kan koma bayan tattalin arziki mafi munin da duniya ta taba fuskanta.

Shugaba Trump dai zai halarci taron, duk kuwa da cewar akasarin kasashen sun amince da zabin Joe Biden.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.