Isa ga babban shafi
Iraqi-Vatican

Fafaroma na son a daina yaki da tsattsauriyar akida a Iraqi

Shugaban Darikar Katolika ta Duniya, Fafaroma Francis ya bukaci kawo karshen tsattsauran ra’ayi da rikice-rikice a jawabinsa  da ya gabatar yau Juma’a a Iraqi, inda yake ziyara irinta ta farko a kasar wadda ta yi fama da yake-yake da kuma annobar coronavirus.

Fafaroma Francis na zantawa da shugabanni addinai da na siyasa a Iraqi.
Fafaroma Francis na zantawa da shugabanni addinai da na siyasa a Iraqi. AP - Andrew Medichini
Talla

Fafaroman mai shekaru 84 ya yi biris da cutar coronavirus da ta sake barkewa a karo na biyu, ganin yadda  ya fito daga  fadar Vatican domin kai ziyarar da aka jima a na dakon ta a Iraqi duk da cewa, ana dari-dari dangane da sha’anin tsaro a kasar.

Manufar ziyarar ita ce, tausasa al’umomin Kirista  masu dadadden tarihi a Iraqi, yayin da kuma ya yi tattaunawa mai zurfi da Musulmai.

Fafaroman ya isa  filin jiragen sama na birnin Bagadaza da yammacin wannan  Jumma’a, inda Ministan kasar, Mustafa al-Kadhemi ya tarbe shi hannu biyu-biyu, yayin da  gungu- gungu na mutanen kasar suka yi ta rare waka da kuma raye-rayen gargajiya don  yi masa lale marhabin da zuwa kasarsu.

Fafaroma ya samu kyakkyawar tarba a filin jiragen sama na kasa da kasa a Iraqi
Fafaroma ya samu kyakkyawar tarba a filin jiragen sama na kasa da kasa a Iraqi AP - Andrew Medichini

 

Tuni jagoran addinin ya gana da shugaban Iraqi Barham Saleh wanda tun a cikin shekarar 2019 ya mika goron gayyata ga Fafaroman.

Kazalika Fafaroman ya tattauna da jami’an gwamnatin kasar da kuma wasu shugabannin addinai.

A jawabinsa da ya gabatar a fadar shugaban kasa, Fafaroman ya jaddada tushen addinin Kirista a Iraqi, yana mai cewa, dadewar Kiristoci a kasar da kuma gudun -mawarsu ta raya al’umma, sun haifar da ginanniyar al’ada da suke fatar ci gaba da wanzuwarta domin amfanin kowa.

A bangare guda, Fafaroman ya bukaci shugabannin kasar ta Iraqi da su tashi tsaye wajen yakar cin hanci da rashawa da amfani da karfin Mulki ta hanyar da ba ta dace ba da kuma rashin mutunta doka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.