Isa ga babban shafi
Easter - Fafaroma

EASTER: Fafaroma Francis ya bukaci samarwa kasashe matalauta rigakafin korona

Shugaban Mabiya darikar Katolika na duniya Fafaroma Francis ya bukaci mabiyan sa da su cigaba da jajircewa, yayin da yake bayyana maganin rigakafin cutar korona a matsayin babban makamin yaki da cutar.

Shugaban tarikar Katolika ta Duniya Fafaroma Francis yayin bukin Easter  a mujami'ar St. Peter's Basilica dake fadae Vatican ranar 4, ga watan Afrelu shekarar  2021.
Shugaban tarikar Katolika ta Duniya Fafaroma Francis yayin bukin Easter a mujami'ar St. Peter's Basilica dake fadae Vatican ranar 4, ga watan Afrelu shekarar 2021. REUTERS - POOL
Talla

Yayin da yake gabatar da jawabin sa kann bikin Easter, Fafaroman dake jagoranci mabiya darikar Katolika sama da biliyan guda da miliyan 300 a duniya ya bukaci ganin an samarwa kasashe matalauta maganin.

Jawabin Fafaroma Francis na bana ya mayar da hankali ne kan annobar korona da marasa lafiya da baki da matsalar tattalin arziki da kuncin rayuwa da kuma mazauna yankunan da ake fama da yaki irin su Syria da Yemen da kuma Libya.

Shugaban mabiya darikar katolikan yace har yanzu annobar korona na cigaba da yaduwa, a daidai lokacin da matsalar tsadar rayuwa da tattalin arziki ke kunar jama’a musamman talakawa.

Fafaroman ya bayyana maganin rigakafin a matsayin babbar garkuwar yaki da annobar inda ya bukaci manyan kasashen duniya da su gaggauta raba maganin zuwa kowanne sako na duniya ciki harda kasashe matalauta.

Har yanzu ana fama da yake-yake a duniya

Shugaban mabiya Katolikan ya kuma ce abin kunya ne har yanzu ana fama da rikice rikicen da ake amfani da makamai, inda ya bukaci kawo karshen yakin Syria wanda yace ya jefa miliyoyin mutane cikin halin kakanikayi da kuma Yemen wanda kasashen duniya suka kawar da kan su akai.

Sakon Faforoma Francis dake nuna damuwa kan yake-yake da ake samu a duniya

Fafaroman ya bayyana goyan bayan sa ga matasan dake bukatar girka dimokiradiya a Myanmar, yayin da ya bukaci tattaunawa tsakanin Isarila da Falasdinawa da kuma kawo karshen tashin hankalin da ake samu a wasu kasashen Afirka da suka hada da Najeriya da Yankin Sahel da Tigray dake Arewacin Habasha da Cabo Delgado dake Mozambique.

Shugaban mabiya darikar Katolikan yace yake yake sun yi yawa a duniya saboda haka ya zama wajibi a dauki matakan kawo karshen su da kuma wanzar da zaman lafiya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.