Isa ga babban shafi
SAUDI-KORONA

Saudiya ta bankado masu sayar da shaidar korona na bogi

Kasar Saudi Arabia ta kama mutane sama da 120 da ake zargi suna hada baki wajen samar da takardun shaidar gwaji ko kuma na karbar allurar rigakafin cutar korona na bogi, kwanaki biyu kafin fara gudanar da aikin Hajjin bana.

Yarima Mohammed bin Salman
Yarima Mohammed bin Salman AP - Mandel Ngan
Talla

Kamfanin dillancin labaran kasar yace daga cikin wadanda aka kama harda jami’an kiwon lafiya guda 9, kuma dukkan su sun amsa aikata laifin da ake zargin su.

Rahotanni sun ce wadanda ake zargin sun yi amfani da kafofin sada zumunta wajen tallata takardun shaidar na bogi da suke sayarwa abinda ya bada damar bankado su.

Rahotan yace daga cikin mutane 21 da ake zargin sun hada kai wajen sayar da takardun shaidar karbar rigakafin, guda 9 Yan kasar Saudiya ne, yayin da 12 kuma  mazauna kasar ne da ake zargi da zama dillalan sayar da takardun.

Dawafi a Dakin Ka'abah lokacin korona
Dawafi a Dakin Ka'abah lokacin korona © AFP - STR

A farkon watan nan hukumomin Saudi Arabiyar sun sanar da kama jami’an kula lafiya guda 2 da ake zargin suna da hannu wajen sauya alkaluman annobar ta korona.

Ana saran jama’ar kasar 60,000 dake dauke da takardun shaidar karbar allurar rigakafin cutar korona su gudanar da aikin Hajjin bana wanda ake saran farawa daga ranar asabar mai zuwa.

Wasu mahajjata a kasar Saudiya
Wasu mahajjata a kasar Saudiya © Rfi hausa - Salissou Isa

Akalla allurar rigakafin cutar korona miliyan 21 aka gabatar wa jama’a a kasar mai dauke da mutane miliyan 34 kamar yadda ma’aikatar lafiya ta sanar.

A jiya laraba gwamnatin kasar ta sanar da samun sabbin mutane 1,226 da suka harbu da cutar, yayin da mutane 14 suka mutu, abinda ya kawo adadin wadanda suka harbu da cutar baki daya zuwa dubu 504 da dari 960, kuma daga cikin su dubu 8 da 20 sun mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.