Yan Sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a Bangkok
Yan Sandan Thailand a jiya asabar sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye tareda harba albarusai na roba wajen tarwatsa dubban masu zanga-zanga da kuma adawa da manufofin gwamnatin dake rike da mulki a kasar.
Wallafawa ranar:
Masu boren na bayyana cewa babu abinda hukumomin suka yi yanzu haka a mataki na dakile yaduwar cutar covid 19 inda alkaluma ke dada nuni cewa kusan mutane 22.000 ne suka kamu da ita a Thailand, 212 sun bakuci lahira.
A daya geffen masu bore na kokawa dangane da tafiyar hawainiya da ake fuskanta wajen yiwa mutane allurar rigakafin kamuwa da wannan cuta,a karshe sun kuma bukaci Firaministan kasar da yayi murabis.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu