Alkaluman mutanen da girgizar kasa ta kashe a Haiti ya kai dubu 1 da 419
Sabbin alkalumma da mahukunta suka fitar na nuni da cewa adadin wadanda suka rasa rayukansu sanadiyyar girgizar kasar da ta afka wa Haiti ranar asabar da ta gabata, a yanzu ya kai mutane dubu daya da 419.
Wallafawa ranar:
Yayin da ake ci gaba da aikin ceto ta hanyar a karkashin tarkacen gine-ginen da suka rufta, zuwa yanzu an tabbatar da cewa sama da mutane dubu 6 da 900 ne suka ramu raunuka, yayin da gidaje dubu 37 suka rushe.
Wasu bayanai na nuna cewa har yanzu akwai sauran mutanen da suka makale a baraguzan gine-ginen da suka rufta, yayinda galibin asibitocin gab da yankin ke makare da masu bukatar agajin gaggawa.
Girgizar kasar mai karfin maki 7 da digo 2 tun a ranakun karshen mako ta afkawa kasar ta Haiti, ko da ya ke ta shafi wasu kasashe makwabta amma tafi barna a cikin Haitin ta yadda ta lalata garuruwa da dama musamman wadanda ke gab da birnin Port-au-Prince da sauran kudancin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu