Isa ga babban shafi
GIRGIZAR-KASA

Girgizar kasa ta kashe mutane 227 a kasar Haiti

Girgizar kasa mai karfin maki 7.2 afkawa kasar Haiti da safiyar wannan Asabar, inda ta kashe akalla mutane 227 tare da rusa gine-gine a cikin kasar har yanzu ba ta murmure daga makamancin bala'in na girgizar kasar da ya afka mat aba a shekarar 2010.

Wani Coci da ya lalace bayan girgizar kasa a yankin Les Cayes, da ke kasar Haiti. Ranar Asabar, 14 ga Agustan, 2021.
Wani Coci da ya lalace bayan girgizar kasa a yankin Les Cayes, da ke kasar Haiti. Ranar Asabar, 14 ga Agustan, 2021. AP - Delot Jean
Talla

Ma’aikatar binciken karkashin kasa ta Amurka ta ce, inda girgizar kasar ta auku na da nisan kilomita kimanin 160 daga tsakiyar Port-au-Prince babban birnin kasar Haiti da ke da cinkoson jama'a.

Hukumar kula da jama'a ta farin kaya tace adadin mutanen da suka mutu ya tashi daga 29 da aka sanar ad farko zuwa 227 sakamkon samun karuwar mutane 158 da suka mutu a yankin kudancin kasar.

Wata matashiya Christella Saint Hilaire da ke zaune kusa da wurin da abin ya faru a yankin kudu maso yammacin kasar, ta shaidawa AFP cewa gidaje, da makarantu da dama sun rushe, a yayin da gwamman mutane suka jikkata baya ga wadanda suka halaka.

An dai ji girgizar kasar da ta dade tana wanzuwa a mafi akasarin yankin Caribbean.

Tuni dai gwamnatin Haiti ta ayyana dokar ta baci don magance bala'in, yayin da kuma wani jami'in Fadar White House ya ce Shugaban Amurka Joe Biden ya ba da umarnin fara ayyukan agaji cikin gaggawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.