Isa ga babban shafi
Haiti - Girgizar kasa

Adadin mutanen da suka mutu a girgizar kasar Haiti ya zarce 700

Ma'aikatan agaji sun dukufa wajen kokarin ceto wadanda suka tsira da rayukansu, da kuma gawarwakin mutanen da suka mutu daga karkashin baruguzan gini a Haiti, bayan da girgizar kasa mai karfin maki 7.2 ta afkawa kudu masu yammacin kasar da safiyar jiya Asabar.

Masu agaji yayin kokarin ciro gawar wata yarinya da daga karkashin baraguzan gidaje, bayan girgizar kasa a Les Cayes, da ke Haiti, a ranar Asabar, 14 ga Augusta, 2021.
Masu agaji yayin kokarin ciro gawar wata yarinya da daga karkashin baraguzan gidaje, bayan girgizar kasa a Les Cayes, da ke Haiti, a ranar Asabar, 14 ga Augusta, 2021. AP - Duples Plymouth
Talla

Kawo yanzu mutane 724 aka tabbatar da mutuwarsu a girgizar kasar da ta rusa dubban gine-gine a kasar ta Haiti, wadda har yanzu ba ta kammala murmurewa daga mummunar girgizar kasar shekarar 2010 ba.

Yadda girgizar kasa ta rusa gine-gine a yankin Les Cayes, da ke Haïti.
Yadda girgizar kasa ta rusa gine-gine a yankin Les Cayes, da ke Haïti. AFP - STANLEY LOUIS

Ma’aikatar binciken karkashin kasa ta Amurka ta ce, inda girgizar kasar ta auku na da nisan kilomita kimanin 160 daga tsakiyar Port-au-Prince babban birnin kasar Haiti da ke da cinkoson jama'a.

Hotunan da aka yada a kafofin intanet sun nuna yadda aka ji girgizar kasar da ta shafe tsawon lokaci tana wanzuwa a mafi akasarin yankunan Caribbean, wadda ta rushe dubban makarantu da gidaje a yankin kudu maso yammacin Haiti.

Hukumar kare fararen hula ta kasar ta ce awanni bayan girgizar kasar adadin wadanda suka mutu na ci gaba da karuwa, inda daruruwan mutane sun jikkata, wasu kuma sun bace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.