Isa ga babban shafi

Mutanen da suka rasa rayukansu a Haiti ya zarta 1300

Sabbin alkaluma da mahukuntan kasar Haiti suka fitar na nuni da cewa adadin wadanda suka rasa rayukansu sanadiyyar girgizar kasar da aka yi ranar asabar da ta gabata a wasu yankunan kasar, a yanzu ya zarta dubu guda da 300.Tuni dai aka kafa dokar ta-baci ta tsawon wata daya, yayin da Amurka ta sanar da tura kwararrun ma’aikatan agaji 65 don gudanar da ayyukan ceto, sai kuma jami’an kiwon lafiyar kasar Cuba da ke taimaka wa wadanda suka samu raunuka

Taswirar kasar Haiti
Taswirar kasar Haiti AFP
Talla

Yanzu haka dai ana ci gaba da gudanar da ayyukan a birnin Les Cayes daya daga cikin yankunan da wannan ifltila’i ya fi shafa a kudancin kasar ta Haiti, inda mutane suka share tsawon kwanaki biyu na samun mafaka a kan tituna.

Aikin ceto a kasar Haiti
Aikin ceto a kasar Haiti AP - Joseph Odelyn

Yayin da a wasu unguwanni ake amfani da manyan motoci don daga buraguzan gine-gine, a wasu wuraren kuwa mutane na amfani da hannayensu ne don daga buraguzan gine-ginen da suka rufta kan jama’a.

Ita dai wannan girgiza kasa da aka yi ranar asabar da ta gabata, karfinta ya kai maki 7 da digo 2 a maunin Ritcher musamman a yankin na Les Cayes mai tazarar kilomita 160 a yammacin Port-au-Prince fadar gwamnatin kasar, birnin da shi ma ya fuskanci irin wannan mumunar girgizar kasar a shekara ta 2010.

Aikin ceto a kasar Haiti
Aikin ceto a kasar Haiti AP - Duples Plymouth

Alkalumma na baya-bayan nan nu nuni da cewa adadin gidajen da suka rufta zai kai dubu 1 da 500, yayin da aka zaro sama da mutane dubu 3 da rayukansu daga cikin tarkacen gine-ginen da suka rufta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.