Facebook ya fara kare jama'ar Afghanistan daga fitinar Taliban
Kamfanin Facebook ya fitar da sabbin matakan tsaro domin kare masu amfani da dandalinsa a Afghanistan bayan mayakan Taliban sun kifar da gwamnatin kasar, yayin da tuni ya dakatar da asusun mayakan.
Wallafawa ranar:
Kamfanin na Facebook ya dauki matakan ne bayan shawarwarin da ya samu daga masu rajin kare hakkin bil’adama da ‘yan jarida da kungiyoyin fareren hula, yana mai cewa, a yanzu masu amfani da shafin a Afghanistan za su iya boye wallafa-wallafansu ga mutanen da su san su ba.
Kazalika, masu amfani da Instagram mallakin Facebook, su ma za su rika samun sakwannin da ke janyo hankulansu kan yadda za su kare asusunsu a kasar.
Shugaban Sashen Kula da Lamurran Tsaro na kamfanin Facebook, Nathaniel Gleicher ya ce, a halin yanzu suna aiki kafa-da-kafa da takwarorinsu na masana’antun fasaha, da kungiyoyin fararen hula da kuma gwamnati domin bayar da duk wani taimako don kare jama’ar Afghanistan.
Mista Gleicher ya kara da cewa, kamfanin na Facebook ya janye tsarin kustawa cikin runbunan wani aboki domin bibiyar jerin mutanen da yake mu’amala da su a shafin a Afghanistan da zummar kare jama’a daga farmakin Taliban musamman ga wadanda mayakan ke fako.
WhatsApp ma dai ya dakile asusun mai magana da yawun Taliban Zabihullah Mujahid.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu