Isa ga babban shafi
LAIFIN-FYADE

Kotu ta umurci wanda ake zargi da fyade ya wanke kayan matan kauyen su

Wata Kotu a India ta bada belin wani mutum da aka tuhuma da laifin yunkurin yiwa wata mata fyade, amma kuma ta umurce shi da ya dinga wanke kayan sawan matan kauyen su gaba daya, yana kuma gogewa na watanni 6.

Firaministan India Narendra Modi
Firaministan India Narendra Modi © AFP - PRAKASH SINGH
Talla

Kotun tace mutumin Lalan Kumar mai shekaru 20 zai dinga sayen sabulun wanki da kudin sa da kuma duk wani abinda ake bukata na wanke kayan domin yiwa mata akalla 2,000 dake kauyen Majhor a Jihar Bihar wanki kyauta.

Santosh Kumar Singh, jami’in Yan Sandan Yankin Madhubani dake Jihar Bihar, yace dama Kumar yana sana’ar wanki da guga ne, kuma an kama shi ne a watan Afrilun da ya gabata, inda aka tuhume shi da laifin yunkurin yin fyade.

Mata a India ke zanga zangar adawa da yadda ake musu fyade
Mata a India ke zanga zangar adawa da yadda ake musu fyade AFP

Dagacin kauyen, Nasima Khatoon yace matan garin sun bayyana farin cikin su da wannan hukuncin, yayin da ya bayyana shi a matsayin mai dimbin tarihi da zai kare martabar mata.

Matan kauyen Majhor sun ce hukuncin zai bada damar mahawara akan laifin cin zarafin su a cikin al’umma da kuma kare martabar su.

Anjum Perween, shugabar wata kungiyar mata, tace umurnin kotun ya zama wani sabon salon da zai aike da sako mai karfi ga jama’a.

A shekarar 2012 aka yiwa dokar fyade a India garambawul amma har yanzu ana ci gaba da fuskantar matsalar, inda a shekarar da ta gabata, mata 28,000 suka gabatar da karar yi musu fyade.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.